Tinubu ya kuduri aniyar kawo karshen matsalar rashin tsaro a kasar nan

0 404

Sakataren gwamnatin tarayya Sanata George Akume, ya ce shugaba Bola Tinubu ya kuduri aniyar kawo karshen matsalar rashin tsaro a kasar nan.

George Akume ya bayyana hakan ne a wajen taron kaddamar da kudirin magance rikicin manoma da makiyaya a jiya alhamis a Abuja.

Sakataren wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa, Chris Tarka, ya bukaci hadin kan dukkanin kowane bangare a sassan kasar nan.

Ya ce babu wanda ya zabi zama dan Najeriya, illa kawai zabi ne daga Allah madaukakin sarki, don haka akwai bukatar a zauna lafiya da juna. Masanin muhalli, wanda ya gabatar da shawarar sa yayin taron Arc. Patrick Ukura, ya ce shi kan sa yana da burin ganin an lalubo bakin warware zaren rikicin manoma da makiyaya wanda acewar sa shi ma hakan ya shafe shi saboda rikicin yayi sanadiyyar kashe abokan karatunsa na firamare su biyu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: