Tinubu ya nemi haɗin kan masu ruwa da tsaki domin a kawo ci gaba mai ɗorewa a Najeriya

0 117

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwanci a Najeriya da su zo a haɗa kai domin a kawo ci gaba mai ɗorewa a ƙasar nan.

Shugaba Tinubu, ya yi wannan kira ne a yammacin ranar Alhamis yayin wani buɗa-baki da ya shirya wa wasu ’yan kasuwar Najeriya a fadarsa da ke Abuja.

Ya ce, bashi da dalilin kasa kawo ci gaba a Najeriya, domin shi ya riƙa yawo yana neman shugabancin Najeriya, don haka babu wani dalili da zai sa yanzu ya ce ya kasa. Tinubu ya ce a lokacin da ya je ziyarar aiki birnin New York na ƙasar Amurka, yayin taron hada-hadar hannun jari a 2023 ya bayyana wa mahalarta taron cewae su ɗauki Najeriya a matsayin babbar ƙasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: