Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya samu nasara a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC da aka gudanar a Jihar Jigawa, inda ya tattara kuri’u 206,520.
Da yake magana kan sakamakon, Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya bayyana cewa wannan nasara wata shaida ce ta amincewar jama’a da manufofin Shugaba Tinubu da kuma ƙoƙarin gwamnatin tarayya wajen bunƙasa tattalin arziki da samar da ci gaba.
Ya kuma jaddada cewa APC a Jigawa na nan tsaf cikin haɗin kai da jajircewa wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar a babban zaɓen shekarar 2027.