Shugaba Trump ya caccaki Birtaniya da sauran kasashen da ke fama da karancin mai saboda yakin da ake yi da Iran.
Ya ce su tashi su ƙwato wa kansu hakki ta hanyar koƙarin buɗe mashigin Hormuz, wadda Iran ta rufe.
Mista Trump ya ce bai kamata su kara tsammanin wani taimako daga Amurka ba, kamar yadda suka ki mara masa baya kan yakin.
Wakilin BBC ya ce fushin da Donald Trump ke yi da ƙawayen ƙasarsa na ƙungiyar ƙawancen tsaro ta Nato ya kai mataki na ƙololuwa a yau, kan jan kafa da suke yi wajen taimakawa a ƙoƙarin buɗe mashigin.
Har yanzu dai ana samun bayanai masu karo da juna game da ko ana tattaunawa don sake bude mashigin.