Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana matsalar tsaro a matsayin babbar damuwar kasar, musamman a yankin Arewa, yana mai cewa wajibi ne a gaggauta dawo da zaman lafiya da haɗin kai.
Tinubu ya yi wannan jawabi ne a Kaduna, ta bakin Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, yayin bikin cika shekaru 25 da kafa Kungiyar Tuntuba ta Arewacin Najeriya (ACF).
A jawabin, ya ce gwamnati na aiki ba dare ba rana domin murkushe ’yan ta’adda, ’yan bindiga da sauran miyagun ƙungiyoyi da ke addabar yankin, suna jefa tattalin arziƙi da ilimi cikin mawuyacin hali.
Ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa gwamnati tana ƙara zage damtse wajen ganin tsaro ya inganta, domin ba za a iya samun ci gaban da ake buƙata ba tare da zaman lafiya ba.