Tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya zargi yan jam’iyyar APC a majalisar wakilai da ta dattawan domin da saba kundin tsarin mulki

0 59

Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamido, ya zargi ‘yan yan Jam’iyyar APC a majalisar wakilai da ta dattawan kasarnan da saba kundin tsarin mulkin 1999 ta hanyar yunkurin tilasta jam’iyyun siyasar kasarnan gudanar da tsarin zaben fidda gwani na ‘yan takara ta hanyar ‘yar tinke.

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kan sa, wanda aka fitar da kuma rabawa manema labarai a Dutse.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadin ya bawa jam’iyyun siyasa yancin gashin kan su.

Ya kara da cewa ya kamata jam’iyyar PDP ta dauki dukkan matakan da suka dace domin kalubalantar wannan kudurin na gyaran dokar zabe a gaban kotu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: