Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta ce kimanin mutane dubu 1 da 547 ne suka harbu da cutar Corona a jiya Lahadi, wanda hakan ne, ya kawo adadin mutanen da cutar ta harba zuwa Dubu 237,561 tun daga 2020.

Daga cikin adadin an samu mutane dubu 212, 550 da suka warke daga cutar kuma aka sallame su.

Haka kuma an bada rahotan cewa cutar ta hallaka mutane dubu 3,022, tun bayan bayyanarta.

Cibiyar ta NCDC ta ce an samu mutanen ne a Jihohi 9 na Kasar nan ciki harda birnin tarayya Abuja.

NCDC ta ce an samu mutane 806 da suka harbu da cutar a birnin tarayya Abuja, sai kuma Lagos mai mutane 401.

Sauran Jihohin da aka samu bullar cutar sun hada da Borno 166, Oyo 78, Ogun 47, Osun 30.

Sai kuma Jihohin Ekiti 7 da Katsina 7 sai Kano 4 da kuma Jigawa 1 da suka harbu da cutar ta Corona.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: