Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce Najeriya ba za ta wargaje ba sakamakon zaben 2023

0 94

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya ce Najeriya ba za ta wargaje ba sakamakon zaben 2023.

Jonathan ya bayyana haka ne a taron kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) na majalisar masana da kuma tsare-tsare da aka gudanar a Legas.

Ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa kan yadda kungiyar ECOWAS za ta iya magance kalubalen da ke fuskantar yankin.

A wani labarin kuma, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce tilas ne Najeriya ta tunkari kalubalen yara fiye da miliyan 13 da ba sa zuwa makaranta a kasarnan, domin magance mummunar matsalar rashin tsaro da kasar ke fuskanta.

Obasanjo ya bayyana haka ne jiya a Abuja a wajen taron shekara-shekara na gidauniyar Murtala Muhammed na bana.

Obasanjo, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Amintattu na Gidauniyar ta Murtala Muhammed, ya bayyana hakan ta hanyar wayar tarho, inda ya kuma jaddada cewa samun dimbin yaran da ba sa zuwa makaranta yana haifar da barazana ga tsaro a nan gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: