Shugaban Kasa Muhammadu buhari ya bayar da shawarar cewa jam’iyyarsa ta APC ta zabi shugabanta na kasa ta hanyar sulhu, ba sai an gudanar da zaben cikin gida ba.

Gwamnan jihar Kebbi kuma shugaban kungiyar gwamnonin APC, Atiku Bagudu ne ya rawaito shugaban kasar na fadan haka a fadar shugaba kasa dake Abuja.

Atiku Bagudu yayi magana a jiya bayan shi da sauran gwamnonin APC sun gudanar da zaman ganawar sirri tare da shugaban kasa.

Atiku Bagudu ya kare matsayar shugaban kasar na neman a zabi shugaban jam’iyyar ta hanyar sulhu, inda yace jam’iyyar ta taba yin hakan a baya.

Gwamnan na jihar Kebbi yace yayi amannar cewa jam’iyyarsa zata cimma manufarta ta samun shugabanni ta hanyar sulhu.

Da aka yi masa tambaya dangane da yadda rikicin babban taron jam’iyyar APC ya raba kan gwamnonin jam’iyyar, Atiku Bagudu yaki cewa uffan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: