Tunji Alausa ya nuna faduwar da akayi a jarabawar JAMB ana yaki da maguɗin jarrabawa a Najeriya.

0 834

Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana cewa raguwar ɗaliban da suka samu maki sama da 200 a jarrabawar UTME ta 2025 wata shaida ce da ke nuna ana samun nasara a yaƙi da maguɗin jarrabawa a Najeriya.

Bisa kididdigar da Hukumar JAMB ta fitar, daga cikin ɗalibai miliyan 1.95 da suka rubuta jarrabawar, kimanin dubu 420 ne kawai suka samu maki sama da 200, lamarin da ya nuna kashi 78 cikin 100 na ɗaliban sun kasa cin jarrabawar.

A wata hira da Channels TV, Dr. Alausa ya ce hakan ya biyo bayan ƙarfafa tsaro da tsarin CBT da JAMB ta saka don hana satar jarabawa, inda ya ce abin ba zai kasance daidai da WAEC da NECO ba.

Ministan ya ce gwamnati na shirin juya jarabawar WAEC da NECO zuwa CBT daga Nuwamban 2025 da nufin magance satar jarrabawa da kuma tabbatar da adalci a fannin ilimi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.