Turkashi: Kashi 20 Na Ƴan Najeriya Na Fama Da Matsalar Hauka

0 153

Gida LabaraiLabaraiLafiyaTurkashi: Kashi 20 Na Yan Najeriya Na Fama Da Matsalar HaukaDaga Amina Hamisu Isa – June 13, 20190 Wani Babban Likita a fannin kwakwalwa da ke asibitin Tarayya a garin Gusau( Federal Medical Center), Dr Aremu Saad ya ce sama da kashi 20 na yan kasar nan, na fama da matsalolin tabin hankali.

Dr Aremu ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke zanta wa da manema labarai a yau alhamis, 13 ga watan Yuni shekarar 2019.Ya ce hakan yana faruwa ne saboda sakacin mutane na rashin zuwa asibi, domin yin gwaji don gane lafiyar kwakwalwarsu.

Ya kara da cewa wannan adadi an same shi ne bayan gudanar da bincike da kwararru suka yi a wannan fanni a cikin wasu shekaru.Daga nan, sai ya kara da cewa acikin mutanen da ke fama da matsalolin tabun hankali, kashi 20 daga ciki ne suke duka ko yin abu mai hatsari.

Sannan, akwai yiwuwar warkewa idan har aka bi ka’idoji da shan magani yadda ya kamata.Haka zalika, ya ce, dalilai da dama na iya janyo matsallolin tabin hankali wanda suka hadar da; sha-shaye, da Gado, da Bakin ciki, da sauransu.

A karshe ya yi kira ga yan Majalisar Tarayya da su sanya hannun akan dokar Lafiyar Kwakwalwa( Mental Health Bill) da zai shafi dukkanin fannin magani, da wurin jiyyar masu fama da matsalolin tabun hankali, da kuma hukunci ga masu aikata laifi ko tsangwaman su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: