Umahi ya ba da umarnin buɗe hanyar Abuja-Kaduna-Kano domin sauƙaƙa tafiyar Babbar Sallah

0 237

Ministan Ayyuka na Najeriya, David Umahi, ya ba kamfanin da ke aikin gyaran hanyar Abuja-Kaduna-Kano umarnin gaggauta buɗe dukkan sassan hanyar domin sauƙaƙa zirga-zirgar matafiya yayin bukukuwan Babbar Sallah.

Umahi ya bayyana cewa matakin na da nufin rage cunkoso da tabbatar da lafiyar matafiya da ke amfani da babbar hanyar a lokacin bukukuwan Eid-el-Kabir.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman ga Ministan kan harkokin yaɗa labarai, Francis Nwaze, ya fitar a ranar Litinin.

Ministan ya kuma tabbatar da cewa an kawar da wani hatsari da ya faru a kan hanyar a baya, wanda ya haddasa tsaikon ababen hawa.

Sanarwar ta ce an umarci kamfanin Infiouest Nigeria Limited da ke aikin hanyar da ya buɗe dukkan wuraren da aka rufe saboda aikin gyare-gyare domin bai wa matafiya damar gudanar da tafiyarsu cikin sauƙi.

Haka kuma gwamnatin tarayya ta tura jami’an tsaro zuwa muhimman wurare a kan hanyar domin tabbatar da tsaro da doka yayin bukukuwan Sallah.

Umahi ya buƙaci masu amfani da hanyar su kiyaye dokokin hanya tare da yin tuki cikin natsuwa domin kauce wa haɗurra.

Leave a Reply