Wasu ƴan fashin daji a jihar Niger sun buƙaci manoma da su biya kuɗaɗen haraji kafin su girbe amfanin gonan da suka noma

0 93

Wasu yan fashin daji a jihar Niger sun bukaci, wasu daga cikin manoman jihar akan su biya kudaden haraji kafin su girbe amfanin gonan da suka noma.

An kuma gano cewa yan bindigar sunyi barzanar lalata amfanin gonan, duk manomin dayaki biyan kudaden kafin girbe amfaninsa.

Anata baganren gwamnatin jihar tayi kira ga al’ummar jihar, akan suyi watsi da bukatar yan bindigar, saboda hakan ya sabawa tsarin hakkin dan kasa.

A cewar kwashinan cikin gida da kananan Hukumomi na jihar Emmanuel Umar gwamnatin jihar a shirye take ta kare rayuka da dukiyoyin manoman dake fadin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: