Wasu kwamandojin Boko Haram da suka mika wuya ga Sojoji sun nemi afuwar ‘yan Najeriya

0 87

Wasu kwamandojin Kungiyar Boko Haram da suka mika wuya ga Sojojin Najeriya sun nemi afuwar ‘yan Najeriya.

A cewar mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu, kwamandojin, ciki har da wani kwararren mai sarrafa bama-bamai, sun mika wuya a jihar Borno, inda rikicin yafi kamari.

Lokacin da aka gabatar da wadanda suka mika wuyan, suna rike alluna dauke da rubutu na rokon gafarar ‘yan Najeriya.

Sojojin sun raba sabbin riguna, kayan abinci, da kayan masarufi ga kwamandojin da suka mika wuya tare da iyalansu.

Kungiyar Boko Haram ta kaddamar da tayar da kayar baya a Najeriya tun daga shekarar 2009, inda ta kashe mutane sama da dubu 50, ta sace daruruwa tare da raba miliyoyin mutane daga gidajensu, musamman a yankin arewa maso gabashin kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: