Gwamnatin jihar Jigawa ta bada wadatattun magungunan rigakafin cutukan dabbobi a Karamar Hukumar Guri

0 57

Gwamnatin jihar Jigawa ta bada wadatattun magungunan rigakafin cutukan dabbobi domin yiwa dabbobin fulanin Karamar Hukumar Guri rigakafi.

Manajan shiyyar Hadejia mai kula da lafiyar dabbobi Mallam Muhammad Abdulkadir ya sanar da hakan a lokacin da ya ziyarci rigagen fulanin.

Muhammad Abdulkadir ya bukaci shugabannin Fulani makiyaya dana manoma dasu hada kai da jami’an rigakafin dabbobin domin samun nasarar aikin.

A wani labarin kuma, an bada kudi fiye da naira miliyan 16 ga mata masu aikin ciyar da dalibai a karamar hukumar ta Guri.

Jamiin kula da shirin yaki da fatara na gwamnatin tarayya a yankin Abubakar Umar Dan Barde ya bayyana hakan ga manema labarai.

Yace mata masu dafa abinchi 150 sun sami kudi naira dubu 100 da kuma naira dubu 80 kowacce.

Leave a Reply

%d bloggers like this: