Sarkin Machina ya bukaci mutanensa da su tabbatar sun saka yaransu a makarantun boko

0 79

Mai martaba Sarkin Machina a jihar Yobe, Alhaji Bashir Bukar Machinama, ya bukaci mutanensa da su tabbatar sun saka yaransu a makarantun boko.

Sarkin ya bayar da shawarar jiya a Machina a wani taron gama gari da masarautarsa ta shirya.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ya bayar da rahoton cewa ana aiwatar da shirin a Kananan Hukumomin Machina da Bade wadanda ke fuskantar karancin yara mata a makarantu.

A wani labarin kuma, Sheikh Usman Suleiman, mataimakin Sheikh Dahiru Bauchi, ya rasu.

Sheikh Usman Suleiman ya rasu a jiya yana da shekaru 76 a duniya, bayan gajeriyar rashin lafiya. Tuni dai aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Dansa, Khadi Mustapha Suleiman, wanda ya tabbatar da rasuwar mahaifinsa ga manema labarai, ya ce an binne shi a Unguwan Kanawa dake Kaduna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: