A Bauchi akalla mutane marasa galihu 500 ne za su amfana da tiyatar ido kyauta

0 88

A Bauchi, akalla mutane marasa galihu 500 ne za su amfana da tiyatar ido kyauta wacce gwamnatin jihar ta dauki nauyi tare da hadin gwiwar wata kungiyar musulmai mai zaman kanta daga kasar Saudiyya.

Gwamnan jihar, Sanata Bala Mohammed Abdulkadir ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da aikin da aka gudanar jiya a asibitin kwararru na jihar da ke Bauchi.

Gwamnan wanda sakataren gwamnatin jihar, Ibrahim Muhammad Kasim ya wakilta, ya ce ana yi wannan karamcin ne don taimakawa marasa galihu da masu rauni a cikin al’umma wadanda ke da matsalar ido amma ba sa iya biyan kudin tiyata.

A nasa jawabin, Wakilin kungiyar, Dakta Murtala Muhammad Umar, ya ce jihar Bauchi na daya daga cikin jahoshi uku da ta ci moriyar shirin a Arewa bayan Gombe da Jigawa, inda ya bayar da tabbacin yin aiki tare da gwamnatin jihar don kawo karin tallafi daga gwamnatin Saudiyya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: