Waani mutun ya mutu a kasar Guinea sanadiyyar kamuwa da ciwon Marburg

0 83

Hukumar Lafiya ta Duniya ta tabbatar da mutuwar wani mutum a kasar Guinea sanadiyyar kamuwa da ciwon Marburg.

Cutar tana haddasa zazzabi mai tsanani da zubar jini da kuma mutuwa a wasu lokutan.

Ana kokarin gano mutanen da ya yi hulda su, domin hana bazuwar cutar mai saurin yaduwa.

Wannan dai shi ne karon farko da aka gano cutar a jikin Bil-Adama a Afirka ta Yamma.

Jami’ai na amfani da tsare-tsaren da aka tanada a kasar Guinea da kasashe makwabtanta na shawo kan barkewar cutar Ebola ta baya-bayan nan domin tunkarar sabuwar cutar ta Marburg.

Hukumar lafiyar ta duniya tace kwayar cutar na da damar bazuwa sosai zuwa gurare masu nisa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: