Yan Bindigar da suka sace Kwamishina a Jihar Niger sun bukaci a biya su Naira Miliyan 500

0 84

Yan Bindigar da suka sace Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labarai ta Jihar Niger Hon Muhammad Idris, sun bukaci Iyalan Kwamishinan su biya su Naira Miliyan 500 kafin sakin sa.

An rawaito cewa yan bindigar sun sa ce Kwamishinan ne a ranar Lahadi a gidansa dake Baban Tunga, dake karamar hukumar Tafa ta jihar, inda suka suke cigaba da tattaunawa da Iyalansa.

A wani Labarin kuma, Gwamnatin jihar karkashin Mataimakin Gwamna Ahmed Ketso sun shirya taron tsaro na gaggawa domin kubutar da Kwamishinan daga hannun yan bindigar cikin gaggawa.

Sakataren Gwamnatin JIhar Ahmed Matane, ya tabbatar da sace Kwamishinan, inda ya kara da cewa hukumomin tsaro suna cigaba da kokari domin kubutar dashi.

Sace Kwamishinan na zuwa ne Mako guda da yan bindigar suka sace Shugaban Jam’iyar APC na shiyar C ta jihar Niger Alhaji Aminu Bobi a gonarsa dake karamar hukumar Mariga ta jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: