Wasu ‘yan bindiga na cigaba da kai hare-hare a kauyukan jihar Filato

0 71

Wasu ‘yan bindiga a jiya da safe sun kai hari kauyuka hudu, da suka hada da Kukawa, Gyanbahu, Dungur da Keram a karamar hukumar Kanam na jihar Filato inda suka da kashe da kuma sace mutane da dama.

An kai harin ne a ranar da rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta karyata jita-jitar da ake yadawa cewa ‘yan bindiga sun kutsa cikin garin Jos kuma za su iya kai hari a kowane lokaci.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ubah Gabriel, a wata sanarwa da ya fitar a Jos, ya ce rundunar ta dauki wani sabon salo na dakile matsalar rashin tsaro a jihar.

Wani mazaunin Kukawa mai suna Adam Musa ya shaidawa maenama labarai cewa da dama sun jikkata yayin da daruruwan mutane suka tsere daga gidajensu sakamakon hare-haren.

Musa ya ce ‘yan bindigar da suka kai hare-hare daban-daban sun mamaye kauyukan ne da misalin karfe 11 na safe inda suka kona gidaje da dama.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ubah Gabriel, baice komai akan lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: