Labarai

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya amince Hukumar Lura da Aikin Malaman Makarantu ta dauki sabbin Malamai dubu 1000 aiki domin su rika koyarwa

Gwamnan Jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya, ya amince Hukumar Lura da Aikin Malaman Makarantu ta dauki sabbin Malamai dubu 1000 aiki domin su rika koyarwa.

Shugabar Hukumar Mrs Na’omi Maiguwa, ita ce ta bayyana hakan, inda ta ce hakan yana cikin matakan da Gwamnan Jihar yake dauka bayan ayyana dokar ta bachi a fannin Ilimin Jihar Gombe.

Haka kuma ta ce amincewar da Gwamnan ya yi na a dauki sabbin Malamai, ya biyo bayan karanci Malaman Makarantu da ake fama dasu a Makarantun Sikandire na Jihar.

Mrs Na’omi ta ce Hukumar ta sauyawa Malamai 288 wuraren aiki kamar yadda suka bukata.

Kazalika, ta ce daukar sabbin Malaman Makarantar ya zama dole biyo bayan hanyoyin inganta Ilimin Jihar Gombe da ake dauka, inda ta kara da cewa wannan shine karon farko a tarihin Jihar na daukar sabbi da sauyawa wasu wuraren aiki su dubu 1,288 a lokaci guda.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: