Gwamnatin Tarayya tace baza a bude miliyoyin layukan waya da aka rufe makon da ya gabata ba, har sai masu layukan sun hada layukan da lambar shaidar zama dan kasa ta NIN.

An sanar da haka cikin wata sanarwa a yau daga hukumar sadarwa ta kasa (NCC).

Hukumar tace sanarwar ta zama tilas bisa yadda aka samu wani shafin internet da ake yadawa a kafafen sada zumunta da wasu shafunkan internet.

Hukumar tace shafin na dauke da labarai da bayanan karya da aka kirkira da nufin yaudarar mutane akan layukan da aka hada kiran waya, saboda rashin hada su da lambobin NIN.

Kazalika, hukumar ta NCC tace masu layukan wayan da basu da lambobin NIN, akwai bukatar suje ayi musu rijistar layi a cibiyoyin da aka ware a kasarnan, daga nan sai su hada layin da lambar NIN ta hanyoyin da kamfanonin layin waya suka bayar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: