Mutanen garin Bauchi suna cigaba da nuna damuwarsu kan hauhawar farashin nama

0 89

Wasu mazauna garin Bauchi sun nuna damuwarsu kan hauhawar farashin nama sakamakon karuwar bukatar kayayyakin da ake samu a wannan watan na Azumin Ramadan.

Binciken da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN ya yi a jiya a kasuwannin Wunti da Muda-Lawal a cikin birnin Bauchi ya nuna cewa farashin ya tashi da kusan kashi 25 cikin dari a cikin mako guda da ya gabata.

Binciken yayi nuni sda cewa ana sayar da kilo na naman Sa akan Naira 2,200 sabanin Naira 1,800 yayin da ake siyar da kafar shanu akan Naira 8,000 sabanin Naira 3,500 kafin azumin Ramadan.

Ana kuma sayar da Kwandon Kwai akan N1,800 sabanin tsohon farashinsa N1,670.

Sai kuma yayin Kaji kilo daya wanda ake siyarwa akan sayarwa N3,500 sabanin N3,000 da aka sayar a kwanakin baya.

Wasu daga cikin mazauna garin da suka zanta da kamfanin dillacin labarai na kasa NAN sun ce tashin wadannan kayayyakin, sun ya jefa su cikin wahalhalu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: