Wasu yan majalissar wakilai 2 sun sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC

0 108

Wasu yan majalissar wakilai 2 sun sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC.

Yan majalissar guda biyu, Lehor Idagbo da Michael Etaba dukkanin su sunfito ne daga jihar Cross River State.

Kakakin majalissar wakilai Femi Gbajabiamila ne ya bayyana ficewar ta su ayau Talata a zauran majalissar.

Ficewar ta su na zuwa ne makonni kadan bayan Gwamnan Jihar River Ben Ayade ya canza sheka daga jam’yyar adawa ta PDP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.

A wani labarin kuma Sanata mai wakiltar Zamfara ta tsakiya Hassan Gusau ya bar jam’iyyar PDP.

Amma babu tabbacin cewa ko Jam’iyyar APAC ya koma.

Shugaban majalissar dattawa ta Kasa Ahemd Lawan ne ya bayyana ficewar sanatan a zauran majalissa ayau talata

A cewar Gusau ya bar jam’iyyar saboda rashin iya gudanar da harkokin demokiradiyya da PDP take fama da shi.

Wannan na zuwa ne kasa da awanni 24 bayan ficewar Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle daga PDP zuwa APC.

Leave a Reply

%d bloggers like this: