Wasu ’yan ta’addar Boko Haram biyu sun miƙa wuya ga sojojin sulke a karkashin shirin Operation Hadin Kai

0 77

Wasu ’yan ta’addar Boko Haram biyu masu alaƙa da juna, Ibn Ali da Ja’afar Abdullahi da suka tsere daga sansanin Boko Haram a Farisu, sun miƙa wuya ga sojojin Birged na 21 na sojin sulke a karkashin shirin Operation Hadin Kai da ke Karamar Hukumar Bama.

Rahoto ya ce ’yan ta’addar sun ajiye makamansu ne a ranar Litinin da ta gabata, a daidai lokacin da dakarun Operation Hadin Kai ke kara ƙaimi wajen ganin sun karkade sauran ’yan ta’addar da ke yankin.

Wannan hali da suka tsinci kansu da kuma fargabar za a kawar da su sakamakon hare-haren da suke kai wa juna a tsakaninsu da bangaren ISWAP, ya sa suka kasance a halin gaba kura baya siyaki.

Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zagazola Makama cewa maharan sun miƙa wuya ne tare da bindigoginsu ƙirar AK47 guda biyu kowace ɗauke da alburusai da wayoyin hannu. Majiyar ta ce ’yan ta’addar da suka mika wuya suna amsa tuhuma daga jami’an soji da nufin tatsar bayanai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: