WHO ta bayar da tallafin rigakafin cutar kwalara miliyan ga gwamnatin jihar Bauchi

0 83

WHO ma’ana Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayar da tallafin rigakafin cutar kwalara miliyan daya da dubu dari biyar ga gwamnatin Jihar Bauchi da ke nan arewacin Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa shugaban hukumar lafiya a matakin farko Dr Rilwanu Mohammed ne ya bayyana hakan a jiya Asabar lokacin da za a fara aikin rigakafin a jihar.

Mohammed ya ce WHO “ta ba mu rigakafi miliyan 1.5 domin tallafa wa matakin Jihar BAuchi na shawo kan wannan annoba.

“Bauchi na cikin jihohi 18 da ke da yiwuwar samun barkewar wannan annoba a cikinsu, kuma cikin gaggawa za a fara aiwatar da wannan aiki a yankunan da suka fi zama masu haɗari,” in ji shi.

Ya ce za a fara ne da kananan hukumomin Dass da Toro da ke fuskantar barazanar cutar.

Mohammed ya kara da cewa za a raba wannan rigakafi kashi biyu ne a yankunan kananan hukumomi.

Ya kuma yi wa WHO godiya a madadin gwamnatin jihar kan yadda hukumar ke taimaka wa wajen shawo kan kalubalen harkokin lafiya kamar dai na wannan annoba.

Wannan rahoton BBCHausa ce ta ruwaito, kuma tayi karin haske gameda yadda lamarin ya afku.

Leave a Reply

%d bloggers like this: