Gwamnatin tarayya za ta gina karin gidajen yari guda 3, masu daukar mutum dubu 3,000 a wasu jihohin Najeriya

0 93

Gwamnatin tarayya ta sha alwashin gina karin gidajen yari guda 3, masu daukar Mutane dubu 3,000 a wasu jihohin Kasar nan saboda rage cunkoso a gidajen yarin.

Ministan Harkokin Cikin Gida Mista Rauf Aregbesola shine ya bayyana hakan a jiya Juma’a lokacin da yake kaddamar da hedikwatar hukumar kula da gyaran hali ta kasar reshen jihar Osun.

Mista Rauf ya ce gwamnati za ta gina gidajen yari 3,000 a jihohin Kano da Rivers da kuma babban birnin tarayyar Abuja.

Ministan ya ce sabbin gidajen Yarin za’a gina su ne tare da Kotuna a jikinsu domin su rika saurarar Karar daurarrun da suke tsare a gidajen.

A cewarsa, dukkan gidajen yarin Najeriya an gina su ne domin daukar fursunoni 57,278, amma kididdiga ta baya bayan nan da aka yi a farkon makon jiya ta nuna cewa akwai fursunoni dubu 68,747, wanda suka kunshi Maza dubu 67,422 da kuma Mata 1,325, Wanda hakan ya zarta ka’ida da kashi 18.

A jawabinsa, Kwanfuturola Janar na Hukumar Prison ta Kasa Alhaji Haliru Nababa, ya yabawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, bisa yada ya warewa hukumar kudude a kasafin kudi.

An sha yin kiraye-kiraye kan rage yawan mutanen da ke daure a gidajen yarin Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: