‘Ya kamata shugaban kasa da gwamnoni su hana auren wuri’ -kungiyar kare hakkin dan Adam

0 92

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta ce auren wuri yana karuwa a kasarnan ne saboda gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi ba su dauki wata doka ta hana shi ba.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce Najeriya ce kan gaba a nahiyar Afirka wajen aurar da yara mata da wuri.

Kodayake dokar kare hakkin yara ta shekarar 2003 da gwamnatin tarayya ta yi, ta haramta aurar da yara ‘yan kasa da shekara 18.

Sai dai jihohin kasarnan da ke amfani da tsarin shari’ar musulunci sun gaza amfani da dokar da gwamnatin tarayya ta yi a kan batun aurar da yara ‘yan kasa da shekara 18.

Leave a Reply

%d bloggers like this: