

Ma’aikatar ilimi a jihar Zamfara ta sanar da sake bude makarantu a yau Litinin.
Cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta sanar da cewa za a bude makarantun firamare da na sakandire a yau.
Kazalika sanarwar ta ce makarantun gaba da sakandire kuma za su kasance a rufe har sai yanayin tsaro ya inganta.
A watannin baya ne aka rufe makarantun jihar saboda matsalolin tsaron da ake ci gaba da fuskanta ciki har da satar dalibai.