Gidauniyar Mallam Adamu Majiya Memorial Foundation ta amince da rangwamen kashi 50 cikin 100 na kudin shiga jamiar Khadija dake Majia ga yan asalin jihar Jigawa da suka cancanta domin yin karatun digiri a shekarar karatu ta 2021 zuwa 2022.

Haka kuma gidauniyar ta yi rangwaman kashi 30 cikin na kudin shigar jamiar ga daliban da suka cancanta yan asalin jihar Kano.

Shugaban gidauniyar Alhaji Musa Adamu Majia ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ga manema labarai a Dutse.

Musa Adamu Majia yace hakan na daga cikin kudirin gidauniyar na bunkasa harkokin ilmi a jihohin Kano da Jigawa da ma kasa baki daya.

Kafin hakan dai Gidauniyar a baya ta sanar da bayar da guraben karatu kyauta ga mazauna garin Majia da suka cancanta su shiga jami’ar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: