Yadda ƴan bindiga suka kashe mutum 38 a jihar Kaduna tareda ƙona gidajen su

0 333

Rahotani daga Jihar Kadunan Najeriya na cewa ƴan bindiga sun kashe mutum 38 a Ƙaramar Hukumar Giwa.

Ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta jihar ce ta sanar da hakan inda ta ce jami’an tsaro sun ba ta rahoton cewa mutum 38 aka kashe a kauyukan Kauran Fawa da Marke da Riheya da Idasu duk a Ƙaramar Hukumar Giwa.

An bayyana cewa ƴan bindigan sun ƙona gidaje da manyan motocin ɗaukar kaya da ƙananan motoci da amfanin gona.

Tuni dai gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya bayar da umarni ga hukumar ayyukan gaggawa ta jihar da ta binciki lamarin da kuma kai ɗauki ga waɗanda lamarin ya shafa.

BBCHausa

Leave a Reply

%d bloggers like this: