Yadda Aka Hangi Shugaban Côte d’Ivoire Ya Kwana A Muzdalifah Tare Da Miliyoyin Alhazai

0 194

Shugaban ƙasar Côte d’Ivoire, Alassane Ouattara, ya kasance cikin miliyoyin alhazai da suka kwana a Muzdalifah bayan kammala tsayuwar Arafah, a wani muhimmin bangare na ibadar aikin Hajji.

An hangi shugaban ƙasar tare da sauran alhazai suna gudanar da ibada cikin tawali’u, ba tare da nuna wani bambanci na matsayi ko mulki ba.

Lamarin ya sake jaddada darasin da addinin Musulunci ke koyarwa na daidaito tsakanin mutane, inda kowa ke tsayawa a gaban Allah Maɗaukakin Sarki ba tare da la’akari da matsayinsa na shugabanci, arziki ko asali ba.

A Muzdalifah, alhazai daga sassa daban-daban na duniya sun hallara a wuri guda domin gudanar da ibadu, tare da tattara duwatsu da za a yi amfani da su wajen jifan Jamara da kuma neman rahama, gafara da yardar Allah Ta’ala.

Masu lura da al’amuran Hajji sun bayyana cewa kasancewar shugabannin ƙasashe tare da sauran alhazai a irin wannan yanayi na nuna haɗin kai, tawali’u da kuma ruhin ibadar Hajji wadda ke haɗa Musulmai daga ko’ina cikin duniya.

Leave a Reply