Yadda aka kama wani matashi da laifin kashe wata yarinyar ‘yar talla tare da binne gawarta a jihar Kano

0 78

Wani da ake zargi mai suna Auwalu Abdulrashid ya amsa laifinsa na kashe wata yarinyar ‘yar talla mai shekara 13 tare da binne gawarta a jihar Kano.

Kakakin yansanda na jihar Kano, Abdullahi Kiyawa, shine ya sanar da haka cikin wata sanarwa.

Abdullahi Kiyawa yace wanda ake zargin ya sace yarinyar inda ya kai wani kango kuma ya doke ta, ya yanka wuyanta tare da binne gawarta a wani karamin kabari da ya haka.

Yace bayan kashe yarinyar, ya kira iyayenta a waya inda ya nemi a bashi kudin fansa na naira miliyan 1.

Abdullahi Kiyawa ya kara da cewa Abdulrashid ya kuma amince da cewa ya taba sace dan’uwar yarinyar dan shekara 3 kuma ya nemi naira miliyan 2 a matsayin kudin fansa.

Yace wanda ake zargin ya saki yaron bayan ya karbi kudin fansa na naira dubu 100.

Leave a Reply

%d bloggers like this: