Gamayyar kungiyoyin arewa a jiya sun ayyana cewa zasu gudanar da zanga-zanga a yau a dukkanin jihoshin arewa 19 dangane da kalubalen tsaro a yankin.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, kakakin gamayyar, Abdul-Azeez Suleiman, yace gammayyar zata hada kan daruruwan matasa a yankin, wajen fitowa kan tituna har sai an biya musa bukatunsu.

Ko a baya ma dai Abdulaziz Suleiman ya soki yarjejeniyar baya-bayannan da aka cimma tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago dangane da karin kudin mai da na wutar lantarki.

Yace matasan za kuma su gudanar da zanga-zanga akan cigaba da kulle jami’o’i saboda yajin aiki.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: