Wasu yara guda biyu mace da namiji masu kimanin shekaru bakwai da tara da haihuwa sun mutu sakamakon wata mummunar gobara da ta tashi a gidansu dake Anguwar Dawaki a garin Suleja ba jihar Neja.

Rahotanni sun kuma nuna cewa mahaifin yaran, Alhaji Alhassan Jibrin Yanji shima ya sami raunuka a kokarinsa na ceto su.

Yanzu haka dai yana can wani asibiti dake garin na Suleja inda yake ci gaba da samun kulawa.

Wani mazaunin anguwar da lamarin ya faru, Bashir Ibrahim ya ce iftila’in gobarar ya faru ne wajen misalin karfe uku na daren ranar Juma’a, bayan da wutar ta kama dakin da suke kwance.

A cewarsa wutar ta kama su ne lokacin da suke bacci, yayin da shi kuma mahaifinsu shima yake dakinsa na daban, amma lokacin da ya farka sai ya ga gidan ya turnuke da hayaki.

Ya ce, “Sai dai abin mamaki a lokacin ma babu wutar lantarki a yankin Dawaki gaba daya, saboda haka har yanzu babu ma wanda ya san musabbabin gobarar.”

Tuni dai aka yi jana’izar yaran ranar Juma’a kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Bashir ya kuma ce ko tsinke ba a iya dauka daga gidan ba sai da wutar ta cinye ilahirin kayan gidan

Shugaban Karamar Hukumar ta Suleja, Alhaji Abdullahi Maje ya tabbatar da faruwar lamarin a hirarsa da wakilinmu ta wayar salula inda ya ce sun kuma dukufa bincike domin gano musabbabinta.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: