Mahara Dauke Da bindigogi Sun Fasa Gidan Yari A Owerri

0 240

Wasu mahara dauke da bindigogi da ababen fashewa sun fasa babban gidan yari da shelkwatar ‘yan sandan jihar Owerri, inda suka saki daruruwan wadanda ke tsare.


Rahotanni daga jihar Imo da ke kudancin Najeriya na cewa wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki a gidan yarin Owerri babban birnin jihar, inda suka saki fursunoni fiye da 1500 da safiyar yau Litinin.

Wata majiya ta ce ‘yan bindigar sun kai farmakin ne tsakanin karfe 1 zuwa 4 na safiyar yau Litinin.

Mahara Sun FasaGidan Yarin Owerri
Mahara Sun FasaGidan Yarin Owerri

Haka kuma maharan sun cinnawa shelkwatar rundunar ‘yan sandan jihar wuta a Owerri, inda suka kona kusan dukkan motocin da ke harabar.

Bugu da kari ‘yan bindigar sun balle tare da sakin dukkan wadanda ake tuhuma da ke ajiye a sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan.

Mahara Sun Cinnawa Shelkwatar 'Yan sanda wuta a Owerri
Mahara Sun Cinnawa Shelkwatar ‘Yan sanda wuta a Owerri

An jiyo maharan suna cewa fursunonin su fice zuwa gidajensu, bayan da suka fasa ginin gidan yarin da wata nakiya da wasu abubuwan fashewa.

Wasu majiyoyi da ke da alaka da hukumar tsaro, sun fadawa jaridar Daily Times cewa, maharan da suke dauke da makamai, sun rera wakokin gwagwarmaya a sha tale-talen fadar gwamnatin jihar, kafin su aukawa wuraren.

Mahara sun kona Shelkwatar 'yan sanda a Owerri
Mahara sun kona Shelkwatar ‘yan sanda a Owerri

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Imo ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta bakin kakakinta Orlando Ikeokwu, duk da yake ba ta ba da cikakken bayani akan harin ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Leave a Reply

%d bloggers like this: