Gobara ta tashi a babbar kasuwar birnin Katsina da ke arewacin Najeriya.

Hotunan da aka rika wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda wutar take rimi.

Ganau sun shaida wa BBC cewa ta tashi ne da misalin karfe 7 na safiyar ranar Litinin ne gobarar ta tashi, inda ta kama shaguna da dama.

Har yanzu dai ba a kai ga kashe gobarar ba.

Kuma ya zuwa yanzu ba a san musabbabin faruwar gobarar ba, da kuma barnar da ta yi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: