Yadda gwamna Badaru na ya karbi mambobin jam’iyyar PDP tsagin kwankwasiyya na jihar Jigawa zuwa APC

0 83

Gwamna Mohammed Badaru Abubakar na Jihar Jigawa ya karbi mambobin Jam’iyyar PDP tsagin Kwankwasiyya a hedikwatar Jam’iyyar APC da ke Dutse babban birnin Jiha.

Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa, Auwal Danladi Sankara, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse.

A cewarsa, Mambobin Kwankwasiyya da suka zo hedikwatar Jam’iyyar a yawansu sun ce sun sauya sheka ne zuwa APC saboda irin halayen Jagoranci da Gwamnan Jihar Jigawa ya nuna tun farkon gwamnatinsa.

Shehu Garu wanda shi ne jagoran tafiyar Kwankwasiyya a jihar Jigawa ya ce aniyarsu ta ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC ya zama dole domin ciyar da Jihar da kasa gaba.

A wani Labarin kuma, Gwamna Mohammed Badaru Abubakar ya kaddamar da zababbun shugabannin Jam’iyyar APC na kasa.

Gwamnan ya yi kira ga ‘ya’yan Jam’iyyar da su dukufa wajen wanzar da hadin kan da ake da shi a cikin Jam’iyyar domin samun saukin cin nasara a zaben 2023 mai zuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: