Yadda hukumar EFCC Ta mama ma’aikatan banki su 12 kan wawushe kudaden jama’a a cikin asusun ajiyar su
Hakumar yaki da ciin hanci da rashawa ta kasa EFCC Ta Kama Ma’aikatan Banki 12 Kan nadar bayanan kwastomomin banki da wawushe kudaden jama’a a cikin asusun ajiyar sun na banki
Rahotanni sun bayyana cewa ababen zargin sun shiga hannu ne tun a ranar Juma’a data gabata.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar, ya bayyana sunayen ma’aikatan bakin 12 da ake zargi da aikata wannan zamba a Jihar Enugu.
Hukumar ta ce binciken farko dai ya nuna ababen zargin sun sace kudaden ne daga asusan ajiyar abokanan huldarsu wadanda suka dade basa hada-hada, saboda tinanin ko watakila mamallakan asusun sun manta ne, sun mutu ko kuma basa da wayo.
Mista Uwujaren ya ce za a gurfanar da ababen zargin a gaban Kuliya da zarar sun kammala bincike.