Aikin kafa kamfanin sufurin jirgin na kasa yanzu haka ya kai kaso 91 cikin 100 – Shugaba Buhari

0 81

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada tabbacin cewa jirgin dakon kaya na Nigeria dayayi alkawarin cewa zaifara aiki kafin ya sauka a mulki, zai fara aiki a watan Disambar wannan shekara.

Shugaban ya bayar da wannan tabbacin ne a taron sake duba ayyukan ministoci karo na uku da aka gudanar yau a babban birnin tarayya Abuja.

A cewarsa, aikin kafa kamfanin sufurin jirgin na kasa yanzu haka ya kai kaso 91 cikin 100.

Ya kara da cewa yanzu haka ana gudanar da ayyukan saukar jirgin a filayen jiragen sama na Legas da Abuja daga hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasa da kasa.

Ya kara da filayen jirgin saman Kano da Fatakwal ma, ana gudanar da irin wannan aikin.

Idan zamu iya tunawa dai an warewa bagaren sufurin jiragen sama na kasa Naira biliyan 14.6 domin gudanar da ayyukan yau da kullum.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa manema labarai cewa tuni gwamnatin tarayya ta karbe jiragen sama 9 daga cikin 20 domin gudanar da shirye-shiryen aikin jirgin Najeriya cikin sauki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: