Jami’an hukumar NDLEA ta kama wasu mutum huɗu da da hannu wajen safarar haramtattun ƙwayoyi a Jihar Legas

0 89

Jami’an hukumar dake yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama wasu mutune huɗu da ake zargi da hannu wajen safarar haramtattun ƙwayoyi masu nauyin Kilogram 16 a Jihar Legas.

A cewar kakakin NDLEA, Femi Babafemi ana zargin mutanen, wanda suka hada da Maza biyu da Mata biyu da safarar ƙwayoyi daga ƙasar Netherlands.

A cewarsa, jami’an NDLEA sun shafe makonni suna bin sawun wani mai suna Aro Aderinde mai shekara 48, inda suka kama shi da zargin shigar da ganyen wiwi mai nauyin Kilogram dubu 3,149 ta hanyar ɓoye shi a cikin ganyen kwakwa wanda aka zuba a Kwantena.

A gefe guda kuma, an kama wasu mata biyu masu suna Hauwawu Bashiru and Basirat Adebisi Yahaya da zargin yunƙurin fitar da wata ƙwaya mai nauyin Kilogram 90.

Bisa haɗin gwiwa da wani fasto mai suna Anietie Okon Effiong mazaunin Jihar Akwa Ibom.

Kuma yanxu haka an guirfanar da su birnin Uyo domin fuskantar shari’a.

Haka kuma, an kama wani da ake zarginsa da dillancin ƙwaya mai suna Monday Michael mai shekara 45 lokacin da yake ɗauke da ganyen wiwi mai nauyin kilogram 365 a birnin Legas

Leave a Reply

%d bloggers like this: