Yadda Jihar Kano Ke Cigaba da Daukar Matakan Kariya Daga Korona

0 115

A wani yunkurin na kiyaye yaduwa cutar numfashi ta Korona, Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umarnin kulle duk makarantun gwamnati a jihar.

A cikin jawabin da kwamishinan ilimi na jihar Muhammad Sanusi Sa’idu Kiru ya rattabawa hannu, ya bayyana cewa wannan kullewa zata fara aiki ne daga ranar Litinin 23 ga watan Maris.

A don haka ne ya ce iyaye sai su tabbatar sun kwaso yayansu daga makaratun kwana nan da zuwa ranar Lahadi.

 Kwamishinan ya kuma ce dawo da yaran da malaman gida zai sa su samu kyakkyawar kulawar da ta kamata musamman yanzu da ake fargabar cutar Korona.

Sai dai ya ce ba an yi hakan ne don cusa tsoro ga mutane ba, sai dai duba da yadda lamarin cutar ke cigaba da bazuwa a duniya wanda haka ke bukatar kulawa matuka.

A don haka ne yayi kira ga iyaye da sauran jama’ar gari da su tababtar suna tsafatace jikinsu da makewayinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: