Kaddara: Gobara Tayi Barna A Kafin Hausa A Jigawa

0 280

Gobara ta kune wani dakin kwanan dalibai a makarantar sakandiren kimiyya dake kafin Hausa a jihar Jigawa. Jami’in hulda da jama’a na rundunar tsaro da civil defence SC – Adamu Shehu ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

Ya ce iftila’in ya afku ne tun a ranar Litinin din 16-03-2020 da misalin karfe 9:45 na dare, wadda ta shafi dakin kwanan daliban da akewa lakabi da sunan Gidan Madaki wanda ke da a kalla kusan dalibai sama da 100 dake kwana a ciki.

Jami’in ya shaida cewa gobarar ta kama ne da talatainin dare a lokacin da mafi yawancin daliban ke sharer bacci, kuma wutar ta lakume duk wani kayan amfani na daliban tare da kone dakin kwanan kurmus.

A cewar Adamu Shehu, babu wani wanda ya samu rauni ko rasa rai yayin gobarar amma sai dai kuma an tafka asarar kayan da ya kai na miliyoyin Naira a dalilin gobarar da har yanzu ba’a kai ga gano musabbabinta ba, sai dai har yanzu ana gudanar da bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: