Ƴan bindiga da aka kyautata zaton Lakurawa ne sun yi wa sojojin Najeriya kwantan ɓauna, inda suka kashe guda 13 tare da jikkata da dama a jihar Kebbi.
Bayanai sun nuna cewa harin ya faru ne a daren ranar Talatar da ta gabata a garin Giro Masa da ke ƙaramar hukumar Shanga, inda dakarun sojin Najeriya ke ƙoƙarin kai ɗauki bayan samun kira da suka yi daga al’ummar garin.
Hukumomi na cewa sojojin da aka kashe 11 ne sai kuma jami’in ɗansanda guda ɗaya sai kuma sauran waɗanda suka rasu da samun raunuka da suka haɗa da fararen hular da suka kasance tsakanin sojoji da Lakurawa yayin musayar wuta.
Kakakin ƴansandan jihar ta Kebbi ya shaida wa BBC cewa ba zai iya cewa uffan ba kan farmakin kasancewar abin da ya faru aiki ne na sojoji.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris ya kai ziyarar gani da ido zuwa wurin da al’amarin ya faru tare da zuwa asibiti domin duba wadanda suka samu raunuka.