Har yanzu tsugune bata kare ba a yankin arewa maso gabashin Najeriya game da batun kawar da matsalar tsaro, kasancewar Gwamnan jihar Borno, kuma shugaban gwamnonin yankin na arewa maso gabas, Babagana Umara Zulum, ya yi shelar cewa ‘yan Boko Haram din da aka yi wa afuwa, sun koma ruwa.

Jagoran mayakan Boko Haram Abubakar Shekaru tare da mabiyansa. Handout BOKO HARAM/AFP/File

A jawabin da ya yi a taron gwamnonin yankin na arewa maso gabas da aka kammala a garin Bauchi, Gwamnan na Borno ya ce ‘yan ta’addan sun canza salo mai matukar hatsari fiye da na baya.

Domin sauraron rahoton da wakilinmu Ibrahim Malam Goje ya aiko mana daga garin Bauchi, sai a latsa alamar sautin dake kasa.

Asalin Labarin:

https://www.rfi.fr/ha/najeriya/20210304-rahoto-kan-yadda-tubabbun-yan-boko-haram-ke-komawa-gidan-jiya

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: