Yadda wani dansanda ya harbe wani dalibi da yaki sanya abin rufe fuska yai daukar fim

0 78

Wani dan sanda a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo a yau ya harbe wani dalibi da yaki sanya abin rufe fuska yayin daukar fim a kan titunan Kinshasa, babban birnin kasar.

Shugaban ‘yan sandan birnin Kinshasa, Janar Sylvano Kasongo, ya shaida wa manema labarai cewa dan sandan da ya aikata laifin, ya gudu kuma ‘yan sandan birnin na neman sa.

Sanya abin rufe fuska wajibi ne a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, inda ake cin tarar dubu 10 na kudin Congo, kimanin dalar Amurka 5.

A Kinshasa, ana yawan zargin ‘yan sanda da cin zarafi da kuma sacekudaden tarar kin sanya abin rufe fuskar da suke karba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: