Masan sun tabbatar da cewa Shisha tafi sigari illa kuma tana jawo kansa da hana haihuwa

0 92

Daga Manuniya

Gamayyar masana kiwon lafiya na ciki da waje sun fitar da gargadin cewa shan Shisha yafi shan taba sigari illa ga lafiya nesa ba kusa ba kuma sunyi ittifakin Shisha na haddasa cututtukan zuciya da jijiyoyin jini da ciwon daji na baki da na ciki da sauransu.

Manuniya ta ruwaito Majalisar kiwon lafiya ta duniya WHO, da cibiyar dakile cututtukan masu yaduwa ta Amurka “American Centre for Disease Control and Prevention” sun yi ittifakin cewa Shisha na haddasa cutar kansar makoshi, da rage karfin maniyyi da ka iya shafar haihuwa, sannan tana kuma kawo cutar huhu ko rage karfin huhu.

Sashin kiwon lafiya na Puch ya ruwaito wani kwararren masanin kiwon lafiya na Jami’ar Ibadan, Dr. Timothy Obembe wanda yace Shisha na dauke da sinadaren toxin masu guba da yafi na sigari illa ga lafiyar jiki.

Manuniya ta ruwaito shima tsohon shugaban kungiyar masana kiwon lafiya ta Nigeria APHPON, Farfesa, Dr. Tanimola Akande yana cewa shisha bata da wani alfanu ga lafiyar jiki sai ma dai illa da take jawowa mai ta’amulli da ita.

Daga cikin illar ta shine tana jefa mutum cikin halin shaye-shayen kayan maye da ta’ammulli da miyagun kwayoyi.

Mista Akande, ya shawarci Gwamnatoci suyi bakin kokarinsu wajen dakile shan shisha da yaduwar ta musamman ganin yadda a yanzu wannan annoba tana neman zama ruwan dare. Yace Gwamnati ta sanya haraji mai tsanani kan masu sayar da Shisha da kayan shishar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: