Yadda wasu ‘yan bindiga sun harbi Ministan Sufuri na Uganda

0 83

Kamar yadda muka samu rahoto daga bbchausa, ‘yan bindiga sun harbi Ministan Sufuri na Uganda, Katumba Wamala, a kusa da gidansa da ke Kampala babban birnin ƙasar.

Shaidun gani da ido sun ce ‘yan bindigar sun isa wurin ne a kan babur.

Janar Katumba Wamala tsohon kwamanda ne a rundunar sojan ƙasar.

Ƙasar ta fuskanci irin waɗan nan hare-hare a ‘yan shekarun nan, waɗanda ‘yan bindiga ke kaiwa a kan babura.

A watan Yunin 2018, an harbe wani shahararren ɗan siyasa mai suna Ibrahim Abiriga a kusa da gidansa, wanda magoyin bayan Shugaba Yoweri Museveni ne.

Tsohon kakakin ‘yan sanda, Andrew Felix Kaweesi, shi ma ta irin wannan hanyar aka kashe shi a Afrilun 2017.

Wannan rahoto yaha yake kamar yadda bbchausa ta rawaito.

Leave a Reply

%d bloggers like this: