Yadda ‘yan sanda suka kama ‘yan fashi da makami guda 9 a Gumel

0 97

Rundunar Yan Sandan Jihar Jigawa ta ce ta kama yan Fashi da Makami 9 wanda suke addabar mazauna yankunan karamar hukumar Gumel ta jihar nan.

Kakakin Rundunar ASP Shiisu Lawan, shine ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN a Dutse a lokacin da yake gabatar da yan fashin.

A cewarsa 4 daga cikin yan fashin, an kama su ne bayan sun kai hari gidan Hajiya Naja’atu dauke da Adduna da misalin karfe 2:40 na safe.

Haka kuma ya ce wasu 4 suma da aka kama, sun amsa laifukansu na fashi da makami.

ASP Lawan Shiisu, ya bayyana cewa sun kama mutane 5 bisa laifin sayen kayan Sata, inda aka karbo wayoyin hannu da kuma kudade kimanin Naira dubu 20,250 daga hannun su.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, ya rawaito cewa yan sandan na cigaba da bincikar mutanen da aka kama kafin gurfanar dasu a gaban Kotu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: