Ana gudanar da aikin ne a garin Sifawa, mahaifar babban hafsan hafsoshin soja, Manjo Janar Faruk Yahya a karamar hukumar Bodinga da kuma karamar hukumar Dange Shuni a lokaci guda.

Da yake kaddamar da aikin a Sifawa a yau, Babban Kwamandan Runduna ta 8, Manjo Janar Usman Yusuf ya ce aikin na daga cikin ayyukan da ake yi domin bikin ranar sojojin Najeriya a jihar.

Ya kara da cewa hakan na nufin inganta alakar sojoji da farar hula, yana mai cewa sai lokacin da al’ummomin da aka yiwa aikin suka samu lafiya sannan za su basu bayanai masu muhimmancin wadanda za su taimaka musu wajen samun nasarar ayyukan.

Hakimin Sifawa, Alhaji Buhari, yayin da yake jinjinawa sojoji kan kokarin da suke yi na maido da zaman lafiya a kasar, ya yi addu’ar Allah ya taimaka musu wajen samun nasara a ayyukansu daban-daban.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: